28/12/2023
ILMIN SHARI'A KAN TUHUMAR LAIFIN CAPITAL OFFENCE
Kun san me ake kira CAPITAL OFFENCE?
Shine laifin da idan aka tabbatar dashi akan wanda ake tuhuma, to za a zartar masa da hukuncin kisa ne ko daurin rai da rai.
To tuhumar kisan kai ta fado cikin Capital Offence.
TAMBAYA
Wace kotu ce take da hurumin yin shari'ar Capital Offence?
AMSA
High Court ko Upper Sharia Court.
Magistrate Court bata da hurumin taɓa Capital Offence.
TAMBAYA
To in haka ne, me yasa ake fara kai masu laifin Capital Offence Magistrate Court tunda basu da hurumi?
AMSA
Kundin tsarin mulkin Nijeriya ya haramta ajiye me laifi a wajen 'yan sanda sama da kwana 2.
To fa!
Sai ga shi an kawo me laifin Capital Offence wajen 'yan sanda. Wanda binciken case din ba zai kammalu a kwana 2 ba.
Meye abin yi?
A irin wannan yanayin, ana daukar wanda ake tuhuma din ne a kai shi Magistrate Court, amma ba don gabatar da shari'ar ba, sai dai kawai don a samu order da za a tsare shi a kurkuku kafin a gama bincike a gurfanar dashi a High Court ko Upper Shari'a Court.
Wannan shi ake kira HOLDEN CHARGE.
AMSA LAIFI
A tsarin shari'a, idan aka je kotu, sai wanda ake tuhuma ya amsa laifin sa, shikenan huta roro, waken gizo ya ƙi 'ya'ya. Sai ayi abinda ake cewa summary trial, a yanke masa hukunci nan take, babu bukatar kiran shaidu.
TAMBAYA
Haka abin yake a Capital Offence?
AMSA
A'a, ba haka bane.
A shari'ar Capital Offence, koda wanda ake tuhuma ya amsa laifin sa, to bisa ƙa'ida ta shari'a dole ne za a rubuta cewa 'ya musanta zargin da ake masa.' Ba a yin summary trial a Capital Offence. Dole ne sai an gabatar da hujjojin da zasu tabbatar da cewa yayi kisan. Na'am, amsa laifin sa yana iya zama shaida.
To haka ake a sharia. Idan kuka ji an ce mai laifi ya musanta zargin da ake masa, ba abinda yake zuwa zuciyar ku ne yake kasancewa ba. Wata ƙa'ida ce ta shari'a wadda dole sai an bi ta.
Mun gode.
Legal Friend Initiative.