27/09/2022
مولد النبي صلى الله عليه وسلم
MAUDU'I NA (1)
CIKAR TSARKIN NASABAR ANNABI
Babu shakka ba kokwanto Allah SWT bai Yi wata nasaba Mai tsarki Kuma mafi tsarkaka ba irin nasabar Annabi Sallahu Alaihi wa sallam, Wanda Yana daga hikimar Ubangiji Subhanu wa ta alaa ya sanya Babu wani da yai tarayya da Annabi Sallahu Alaihi wa sallam a wajan haihuwa iyayensu shi kadai s**a Haifa sabida ya tabbatar da cikar nasabar Annabi da Kuma cikar daukakarsa.
Allah Subhanu wa ta alaa Yana fada acikin Alqur'ani Mai girma cewa:
الذى يراك حين تقوم وتقلبك فى الساجدين
Maana: shine sarkin da yake ganinka a lokacin da kake mikewa (yayin ibada), Kuma shine sarkin da yake ganin jujjuyawarka (ciratuwarka) a cikin masu sujjadu.
Anan Abdullahi Dan Abbas yake cewa abin da Allah yake nufi ai من نبي إلى نبي حتى أخرجك نبيا tun daga Annabi izuwa Annabi har Allah ya fitar da Kai kana matsayin Annabi.
Idan mukai duba izuwa wannan ayar tana tabbatar mana da cewa duk Wanda yake cikin zirin nasabar Annabi dukkan su masu sujjada ne ga Ubangiji daga Annabawa sai manyan bayin Allah kamar yadda Allah ya tabbatar mana a wannan ayar.
An Sami Hadisi daga sayyadina Anas RTA yace: Annabi Sallahu Alaihi wa sallam ya karanta fadin Ubangiji لقد جاءكم رسول من أنفسكم ya karanta da yiwa "fa'un" fataha, a maimakon "rufua" maimakon "anfusukum" sai ya karanta da fataha "anfasukum" sayyadina Anas yace da Annabi ya karanta sai yace: أنا أنفسكم نسبا وصهرا وحسبا ليس في آبائ من لدن آدم سفاح "nine mafi tsadarku, mafi darajarku a nasaba (nasaba ta duk tafi taku) mafi darajarku a sirikantaka, mafi darajarku a dangane, Babu wani abu na zubar ruwan ban zan jahiliyya acikin iyaye na tun daga Annabi Adamu".
Daga nana Aisha RTA tace: daga Annabi Sallahu Alaihi wa sallam daga mala'ika Jibrilu Alaihis salam yace: na caje mahudar Rana da mafadarta ban ga wani mutum Mai girman daraja irin Annabi Sallahu Alaihi wa sallam ba, Kuma Banga wani dangi mafi daraja da girma ba irin dangin banu Hashim.
Zan tsaya a Nan sai mun hadu a maudui na