Bãr Adãm Gombe

Bãr  Adãm  Gombe Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Bãr Adãm Gombe, Legal, Tudun wada shamaki, Gombe.

Ko Kasan tanade-tanaden da Kundin tsarin dokokin Nijeriya na Shekarar 1999 yayi akan Ilimi ?____________________________...
04/01/2023

Ko Kasan tanade-tanaden da Kundin tsarin dokokin Nijeriya na Shekarar 1999 yayi akan Ilimi ?
_____________________________________________

Ilimi abune mai matukar muhimmancin da baya bukatar a zauna a bayyana maka amfanin sa, ko kuma illar da rashin sa yake haifarwa, hakan ne ma ya sanya Kundin tsarin dokokin Nijeriya na Shekarar 1999 yake da kyakyawar manufa akan sa, zamu fahimci hakane idan muka kalli Sashi na 18, Babi na II (Section 18, Chapter II) na Kundin Tsarin Mulkin kasar.

Ga tanade-tanaden da Constitution din yayi kamar Haka:

1• Sashi na 18 kashi na daya (Section 18, Subsection 1) ya bayyana cewa:
“Gwamnati za ta mayar da hankali wajen ganin an bayar da damar samun ilimi kowane iri ne, kaɗan ko mai yawa a kowanne mataki”

2• Sashi na 18 Kashin na biyu (Section 18, Subsection 2) ya bayyana cewa:
“Gwamnati za ta haɓɓaka ilimin kimiyya da fasaha”

3• Har ila yau, Sashi na 18 dindai Karamin kashi na uku ya bayyana cewa:
“Gwamnati za ta tashi tsaye wajen ganin ta kawar da jahilci a duk lokacin da ta ga ya dace ta hanyar:

(a) Bayar da ilimin firamare kyauta tare kuma da mayar da shi tilas a kan kowane ɗan Najeriya.

(b) Bayar da ilimin Sakandare Shima kyauta.

(c) Bayar da ilimin jami’a kyauta.

(d) Buɗe ajujuwan yaƙi da jahilci.

Wadannan sune tanade-tanaden da Kundin tsarin dokokin Nijeriya na Shekarar 1999 yayi akan Ilimin Kasar.

Bissalam
Bar adam gombe

Address

Tudun Wada Shamaki
Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bãr Adãm Gombe posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share