Mimbarin sunnah

Mimbarin sunnah Sunnah sark

26/12/2025

_🌹🌹An kar6o daga Anas رضى الله عنه yace :Manzon Allah ﷺ yace :  Alqiyamah ba za ta tashi ba, har sai mutane sun fara gas...
07/12/2025

_🌹🌹An kar6o daga Anas رضى الله عنه yace :Manzon Allah ﷺ yace : Alqiyamah ba za ta tashi ba, har sai mutane sun fara gasar gina masallatai.🌹🌹_

Ibn Majah da Wasunsa.

_🌹🌹Manzon Allah ﷺ yace : Idan Allah ya baka dukiya, to aga alamar ni'imar Allah da karamcinsa a tare da kai.🌹🌹_ Ahmad
07/12/2025

_🌹🌹Manzon Allah ﷺ yace : Idan Allah ya baka dukiya, to aga alamar ni'imar Allah da karamcinsa a tare da kai.🌹🌹_

Ahmad

🛑 *SANARWA GA 'YAN UWA MASU ALBARKA* 🛑Don Allah a kiyaye ɗora hotuna da fina-finan batsa a kafafen sada zumunta. Wannan ...
07/06/2025

🛑 *SANARWA GA 'YAN UWA MASU ALBARKA* 🛑

Don Allah a kiyaye ɗora hotuna da fina-finan batsa a kafafen sada zumunta. Wannan aiki yana haddasa yaduwar alfasha da sabawa Allah a bainar jama'a.

📝 Har ila yau, a kula da duk abin da za a rubuta ko a tura. Lallai mutum zai fuskanci hisabi a kan kowanne abu da ya wallafa ko ya tura – ko da a sirrance ne ko a fili.

📖 Ka tuna:

> "Babu kalma da mutum ke furtawa face akwai mai lura da ita – yana rubuta ta."
(Surat Qaf: 18)

⛔ Ka guji wallafa abin da zai jawo zunubi a gare ka ko ga wasu.

07/06/2025

NASIHA: KI RIKE MUTUNCIN KI, ‘YAR UWA MAI ALBARKA.
-
‘Yar uwa mai albarka, ki sani cewa mutuncin ki daraja ne da Allah Ya azurta ki da shi. Idan kin bar shi ya zube, ba kowa zai iya dawo miki da shi ba kamar da. Ga wasu nasihohi da za su taimaka miki wajen kiyaye mutuncin ki:
-
01. Ki Kiyaye Tsakanin Ki da Allah
Ki kasance mai tsoron Allah a boye da bayyane. Wanda ke da tsoron Allah zai kiyaye kansa daga aikata abin da zai bata masa suna.
-
02. Ki San Darajar Kanki
Kada ki bari wani ya wulakanta ki, ya raina ki ko ya dauke ki kamar abin wasa. Ki san darajar ki, ki dauki kanki a matsayin mace mai girmamawa da kima.
-
03. Ki Tsare Kanki da Kayan Sutura Masu Kariya
Ki rufe jikinki da sutura mai kyau wacce za ta kare ki daga kallon banza da hadurran zamanin nan.
-
04. Ki Kiyaye Hulɗarki da Maza
Kada ki kusanci maza da halaye ko maganganu da za su iya zubar da kimarki. Ki kasance mai tsari da hankali a duk lokacin da k**e mu’amala da su.
-
05. Ki Kare Martabar Iyalinki
Mutuncinki ba naki kadai ba ne yana da nasaba da iyayenki, mijinki (idan kina da aure), da al’ummar da kika fito. Ki zama abin alfahari garesu, ba abin kunya ba.
-
06. Kada Ki Rika Bayyana Sirrinki ga Kowanne Mutum
Sirrinki ne mutuncinki. Idan kin rinka fadawa mutane halayenki ko abubuwan da k**e ciki, zai iya janyo sharri ko zubar da kimarki.
-
07. Ki Kasance Mai Hakuri da Natsuwa
Mutunci yana zuwa da hakuri da sanin ya kamata. Kada ki mayar da martani cikin hanzari idan an bata miki rai. Ki nuna hikima da hankali.
“Wanda ya rike mutuncinsa, Allah zai daga darajarsa. Amma wanda ya wulakanta kansa, to duniya ma za ta wulakanta shi.”

Allah Ya sa mu dace da wannan nasiha.

Allah Kabamu Ikon Zuwa ✅
06/06/2025

Allah Kabamu Ikon Zuwa ✅

Address

Gombe

Telephone

+2347046949568

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mimbarin sunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mimbarin sunnah:

Share

Category