Nagarta youth development association - nyda bauchi

Nagarta youth development association - nyda bauchi Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Nagarta youth development association - nyda bauchi, Legal, JANRUWA DAWAKI WARD BAUCHI, Bauchi.

23/03/2026
GCDSS OLD STUDENT 2021/2026
23/03/2026

GCDSS OLD STUDENT 2021/2026

YANZU-YANZU: CHINA TA GARGADI AMURKA KAN SHIGA LAMURAN NIGERIAGwamnatin Kasar China ta gargadi Gwamnatin Amurka da ta da...
04/11/2025

YANZU-YANZU: CHINA TA GARGADI AMURKA KAN SHIGA LAMURAN NIGERIA

Gwamnatin Kasar China ta gargadi Gwamnatin Amurka da ta daina saka baki cikin harkokin cikin gida na Nigeria.

A yayin taron manema labarai a yau, Mao Ning, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, ya bayyana cewa kasar su tana goyon bayan hadin kai da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da jaddada cewa ba daidai ba ne kasashen waje su yi amfani da addini ko siyasa wajen tsoma baki cikin lamuran wata kasa.

Mao Ning ya ce:

> “China tana adawa da duk wani nau’in katsalandan da ke amfani da addini ko dalilan siyasa wajen shiga cikin harkokin cikin gida na kowace kasa, musamman Nigeria.”

Ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan kalaman shugaban Amurka game da yanayin tsaro da addini a Najeriya.

---

🟢 “Girmama ikon kasa da mutuncinta shine ginshiƙin zaman lafiya da haɗin kai a duniya.”

✍️ Comrade Ibrahim Jarruwa

🌑 MATSALAR SHAYE-SHAYE A CIKIN MATASA 🌑A yau ɗaya daga cikin manyan bala’o’in da ke cinye makomar matasa shi ne shaye-sh...
03/11/2025

🌑 MATSALAR SHAYE-SHAYE A CIKIN MATASA 🌑

A yau ɗaya daga cikin manyan bala’o’in da ke cinye makomar matasa shi ne shaye-shaye da lalata.
Wasu matasa suna ɗaukar shan waɗannan abubuwa a matsayin salo ko nishaɗi, amma a zahiri hanya ce ta rushewar rayuwa da lalacewar hankali.

Ana shan abubuwa iri-iri kamar Wiwi, Kana da, Kolo, Taba, Sh**ha, Barasa, Tramadol, Codeine, Ice, Crack, K2 (Spice), Molly, Ecstasy, Va**um, da wasu ƙwayoyi masu lakabi daban-daban da ake ƙirƙira kowace rana.
Duk waɗannan abubuwa suna lalata kwakwalwa, suna rusa mutunci, kuma suna iya jefa mutum cikin cuta ko ma mutuwa.

Matashin da ya rungumi shaye-shaye, yana cutar da kansa fiye da yadda yake tunani.
Zai rasa natsuwa, hankali, da girmansa a idon iyaye da al’umma.
Wasu har suna zama kaya a hannun iyayensu — ba su da amfani, sai dai bakin ciki.

Matasa, ku tuna: duniya tana kiran ku da kyakkyawar rayuwa, amma shaye-shaye suna kira ku zuwa halaka.
Ka guji abokai masu kawo maka irin waɗannan abubuwan, domin su ne hanyar farko ta lalacewa.

Rayuwa tana da kyau idan aka rayu da tsoron Allah, da neman ilimi, da sanin darajar kai.
Ka zaɓi nagarta, ka guji barna, domin kai ginshiƙin gobe ne.

🕊️ Ka nisanci shaye-shaye — domin mutum mai hankali baya shan abin da ke kashe shi a hankali.

✍️ Comrade Ibrahim Jarruwa

Address

JANRUWA DAWAKI WARD BAUCHI
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nagarta youth development association - nyda bauchi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category