19/08/2026
MATSAYIN ƊALIBAI KAN ALƘAWARIN DA AKA YI MUSU
SASHI NA FARKO
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.
Ina mai gabatar da godiya da jinjina ta musamman ga Shugaban Karamar Hukumar Sabuwa, bisa irin ƙoƙarin da yake yi wajen cigaban al’umma, musamman a fannin ilimi da walwalar ɗalibai. Hakika, mun shaida ana ƙoƙari sosai, kuma wannan abin a yaba ne.
Kamar yadda kowa ya sani, a ranar 03/03/2026, mun samu karramawa daga Shugaban Karamar Hukumar, inda ya zauna da shugabannin ƙungiyar domin sauraron koke-koken ɗalibai da fahimtar ƙalubalen da suke fuskanta.
A wannan zama, Alhamdulillah, an saurare mu, sannan muka gabatar da wasu muhimman buƙatun ɗalibanmu. Waɗannan buƙatu ba wai na ɗalibai kaɗai ba ne; abubuwa ne da idan aka aiwatar da su za su taimaka wajen gina ɗalibai da ƙara wa al’umma cigaba.
Alhamdulillah, an amsa mana kuma aka yi mana alkawarin cika waɗannan buƙatu.
Kamar yadda aka sani, duk mai buƙatar taimako yana da lokacin da taimakon ya fi muhimmanci, domin a lokacin ne zai fi amfani wajen magance matsalar da yake fuskanta.
Haka abin yake ga ɗalibi. Ɗalibi ba mai sana’ar roƙo ba ne; neman tallafi yake domin ya samu damar tsayawa da ƙafafunsa, ya kammala karatunsa, sannan ya zama mai amfani ga kansa da al’ummarsa.
Saboda haka, muna matuƙar yaba wa Shugaban Karamar Hukumar bisa sauraronmu da kuma nuna shirin tallafa wa ɗalibai.
Allah Ya ƙara masa ƙarfin guiwa, Ya taimake shi wajen cika duk wani alƙawari da zai amfani ɗalibai da al’umma baki ɗaya.