03/08/2025
🛑 Shin Dan Sanda Zai Iya Kamaka Saboda Kana Waje da Dare?
❌ Amsar Gaskiya: A’a – Fitowa da Dare Bai Zama Laifi ba a Najeriya.
Babu wata doka a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulki na 1999 ko dokokin ƙasa da ke haramta yin tafiya ko fita da dare — matuƙar ba ka aikata wani laifi ba.
⸻
✅ Yaushe Ne ‘Yan Sanda Zasu Iya Kamaka Da Dare?
• Idan Ana zargin ka aikata laifi (misali sata, kai hari, ko shan miyagun ƙwayoyi).
• Idan ka ƙi bayyana kanka ko ka ƙi bada haɗin kai.
• Idan kana cikin yanki da aka saka dokar hana fita (misali lokacin rikici, ko dokar kulle).
• Idan an karɓi ƙorafi ko rahoto a kanka.
⸻
❌ Amma Ba Za Su Iya Kamaka Saboda Wadannan Ba:
• Saboda kawai kana yawo da dare.
• Saboda irin tufafinka ko salonka.
• Saboda kawai suna ganin “kana da k**a da wanda ake zargi” ba tare da hujja ba.
⸻
📜 Haƙƙinka a Karkashin Doka:
• Sashe na 35 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya tabbatar maka da:
• ‘Yancin yin yawo a kowane lokaci.
• Ba za a k**a ka ba sai da hujja.
• Dole ne a gaya maka dalilin k**a ka.
⸻
🧠 Me Za Ka Yi Idan Aka Tsayar da Kai da Dare?
1. Ka kwantar da hankalinka, kada ka yi gardama.
2. Ka tambaya cikin ladabi:
“Dan sanda, menene dalilin k**ani, shin na aikata wani laifi ne?”
3. Idan babu laifi da aka bayyana, ka ce:
“Da girmamawa, fitowa da dare ba laifi bane. Ina da haƙƙi a ƙarƙashin Sashe na 35 na Kundin Tsarin Mulki.”
4. Idan kaga ana Neman zaluntarka, idan kana da Lauya ka kirashi ko ɗan uwa nan take.