10/10/2025
A'a Bala Lau !
Babu Wani Ahlussunnah da yake Kan Wanan Munanan malaman Ɓatanci da aka Kwatanta Annabi Alaihis Salam da su...
Da dai cewa Kai Dukkan Ku Ƴan Izala to da ya fi kusa da mu gane mu Yarda, kuma da ya ƙara mana karfin Gwiwar Danganta Raini ga Annabi da Rashin Ganin Girman sa da Kuke yi.
Kuma cewa Dukkan Ku shima Karya ne da Rashin Adalci, tun da Mun ji wasu da dama a cikin Ƴan Izala da s**a Barranta Kan su, Kuma s**a Tabbatar da Cewa ba za su fifita ba wa Masoyin ku Triumph kariya fiye da Haƙƙin Sayyidu na Rasulullahi da ya taɓa ba, ya yi (Su'ul Adab) Ko (Kuskure) ba, Kamar dai yadda Su s**a faɗa.
Kuma muna Roƙon duk Wanda da Gaske Yana tare da Lafuzan Triumph, to Dan Allah ya fito fili ya Nanata Lafuzan yadda ya faɗa kwabo da kwabo, Dan ya tabbatar mana da gaske Shi ma yana tare da shi ɗin da Gaske.
Mun faɗa mun Nanata, ba Maganar Hadisi ya Inganta ko bai Inganta muke ba, Maganar danganta Miyagun Misalai na Raini tare da Sunan Sayyidu na Rasulullah Muke, Kuma kowa ya ji Kalaman nan ya gane da kyau. Kuma Duk Masoya da Masu Ganin Girman Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam sun kuskuranntar sunyi Allah wadai, Saboda haka tada Jijiyar Wuya da Barazanar Wai su wane Suna Akai, yana nufin Wannan su wane ɗin Sun Raina Manzon Allah ba sa Ganin Girman Manzon Allah, Kuma Idan Gama garin Al'umma Suna muku Tambari da Makiya Annabi to ku ne ku Sahhale musu, ku ka ba su Ƙofa.
Ni na Tabbata Wallahil Aziim, Babu Wani Malamin Izala da zai ji Lafuzan nan da ake Zargin Triumph Akai, face sai a ran sa ya Tabbata kuma ya gane cewa Lallai Wannan Lafuza suna ɗauke da Ɓatanci ko kuskure ko Su'ul Adab ga Ma'aiki, Amma tsoron kar a kwayewa Dan uwa baya, ko tunanin kar a Taya ƴan Darika baiwa Annabi kariya sai su hana shi Bayyana Gaskiya.
To shin Fifita soyayyar Dan Ƙungiya, Ko Gudun Tarayya da Ɗan Ɗarika, Ya Isa Uzurin a Wofintar da Hakkin Manzon Tsira?
Sallallahu Alaihi Wasallam..
Shehi Mai Jamaa