26/09/2023
Shawarwari garemu Yan Ashabul Kahfi daga rubutun Adam Abumajid Abu Baqara:
YAKAMATA DAN AS'HABUL KAHFI YASAN.....
duk wani yaqi an Gama yi masa shi, sannan duk wata dabara an rubuta masa an a jiye , na shi kawai ya dauko ya bibiya daga tarihi hanyar da aka bi aka yi Nasara ya sabunta ta sannan ya dauka, wacce aka yi kuskure a waccan tafiyar shi kuma ya gyara a cikin ta shi tafiyar,
Yak**ata mu Dan yi duba izuwa wasu Qarinoni da s**a faru Akan idanun duk wani Dan ashabul kahfi in dai ba qasa da shekaru 16 yake ba a halin yanzu da nake yin wannan Maganar!
A kwai wasu aiyukan Alheri da sheikh Abduljabbar (h) ya assasa su bai k**ata ace sun tsaya ba domin baya nan! , duk da Rawiyoyi da halqoqi sun yi qoqari wajen raya zikirin riyadul jannah kuma yanayin Armashi , Amma da zasu za6i wata rana guda daya su shirya taron zikirin na qasa a madadin taron khatama da shi sheikh Abdallah din ya assasa da sun Girgiza teburin... NUFUZIN su ya ci gaba da Qaruwa kuma abokan Gabar su zasu kasa bacci k**ar yadda s**a hana muku bacci , k**ar yadda yan uwa almajiran sheikh mazloom Ibrahim Yaaqoub El zakzaky (h) s**a ci gaba da raya tattaki na yaumul arba'in, duk da wanda suke zuwa wajen sa domin jaddada bai'ar su gare shi bayanan wannan ma ba umarnin sa ba ne daga baya umarnin shi yazo,,
Be k**ata irin kyaututtukan da sheikh Abduljabbar ya saba yiwa masu raunin cikin almajiran sa ta tsaya bayan baya nan ba, k**ar yadda almajiran sheikh El zakzaky s**a ci gaba da Rabon kayan abinci ga wadanda shehun malamin yake yiwa wasu al'ummar tun kafin akai ga zalintar sa,,
Shi fa ku gane wannan,!! yan uwa yan ashabul kahfi, Kiran wadannan bayin Allahn ba wai kira ne na yin fito na fito da shugabanni ba! A'a kira ne da yin fito na fito da zalinci, duk wanda Ka gani yana matsayin shugaba Amma yana kallon wadannan shehunan malaman a matsayin barazana! believe me! Azzalumi ne, Da baya zalinci babu Abinda zai saka shi ya tsargu! Me yasa adalan shuwagabannin basu da irin wannan barazanar? Fitowa domin yin tattaki na lumana ba yana nufin Kun fito ku ja layi da shugabanni ba ne, A'ah illa iyaka zaku tunawa shugabanni ne cewa Ana zalintar ku, kuma Alhali kuu ma yan qasa ne k**ar kowa! , Ina son muridai su San wannan,
sannan ba ko yaushe ne ake jiran umarnin jagora ba kafin aiwatar da Abinda yake daidai ne ko wanda ya dace , a 6angaren yan uwa almajiran Malam (h) FIKIRAR Abuja struggle ba umarnin Malam aka jira ba lokacin da aka soma wannan sabuwar gwagwarmayar, kuma Babu shawarar sa domin lokacin da aka fare ta babu wanda ma yasan inda shehun malamin yake cikin almajiran shi, ga shi kuma kwalliya ta biya kudin sabulu,
Sannan k**ar ita kan ta harkar tsaron jagora ba'a buqatar umarnin shi a wasu lokuta domin a ba shi kariya, saboda shine ( risalar) gaba dayan ta, Idan an kashe shi to k**ar an qone muku littafin risalar ku ne wanda kuma shine kadai ya mallake shi,
Jagora k**ar birni ne masu tsaron shi kuma sune ganuwar birnin , babu hikima cikin tunanin Ka bawa jagoran Ka ran Ka! dai dai yake da an karya ganuwar wancan Garin Don haka sai Abinda birnin ya gani daga wulaqancin abokan gaba!
Shi jagora kana hana kan Ka mutuwa ne Ka kuma yi duk yadda zaka iya domin ba shi kariya Ka hana me cutarwa isa gare shi, ina dabara ga wanda yake da damar tsira tare da jagoran shi Amma kuma Ka tsaya mutu su Ka isa gare jagoran na ka? , Idan abokan gaba sun taso ku gaba a filin yaqi burin su Idan sun kashe jagoran ku to sun karya ku, anan shi jagora zai fada muku ne ku tsaya kuyi Shahada saboda shi yana da total submission ne zuwa ga Allah, aljannah kawai yake kallo a wannan lokacin, , Amma ku masu tsaron sa Kun San cewa rayuwar sa muhimmiya a gare ku, Idan Kun rasa shi Kun rasa komai bayan ku zata 6al6alce, Don haka yanzu dauke shi ku 6oye shine wajibi a kan ku koda kuwa shi bai amince muku da yin hakan ba! Shaikh Nasrallah shine shugaban muqawamar da yafi kowa dadewa a raye domin sirrin hakan shine ya bar Jami'an tsaron shi suyi duk kan Abinda ya dace su yi domin kare shi,
Yaushe ne masu mumbari Akan social media na ashabul kahfi s**a ta6a shiryawa kan su taro gaba dayan su s**a halarta domin tuntu6ar juna,?
Ina aka kwana? Meye motsin mu na gaba? Wataqila suna yi Amma a daidaikun su, shima wannan yak**ata Su dauki darasi daga taron mu'utamar da almajiran sheikh El zakzaky suke shiryawa junan su lokaci zuwa lokaci kuma ko meye ke gaban mutum na uzuri s**an bari suje su halarci taron domin muhimmancin sa, wannan ya sanya hatta bayan malamin yana hannun azzalumai ku Ka GA memakon abin Yayi baya sai ma almajiran shi s**a sake samun sabon yaqini,
ba da addu'ah kadai s**a yi galaba ba, sai da s**a hada da sa'ayi tare da amfani da gwagwarmaya irin wacce azzalumi yake yi musu amfani da ita, BARAZANA su ba sa tsoron ta! KISA ba sabon Abu bane a gare su, su din tamkar FALASDINAWA NE A YAYIN INTIFADA! ku tuna cewa sheikh Abduljabbar ya ta6a yi muku wani karatu na BIDANATAINI ya kuma fada muku cewa duk kan annabi yana tare da su, da masu ba shi shawara ta gari, da masu ba shi shawara ta sharri, masharrantan cikin na shi sune masu amfanuwa da tsare shi da hukumomi suke yi, ku lura da wannan!
Bana wakiltar yan uwa almajiran Malam zakzaky (h) a wajen rubutu, haka kuma bana wakiltar yan'uwa almajiran sheikh Abduljabbar (h) a rubutu, abinda zai amfane ku cikin Abinda na fada ku dauka kuskuren ciki ku taya ni roqar Allah ya yafe mini bidi'o'in ciki ku bar mini Ka yana, fahintar shehu Timothy ce haka!