29/08/2026
🌿 SABEEL FOUNDATION
📖 Hadisin Yau
قال رسول الله ﷺ:
«أَنَا وَكَافِلُ الْيَتِيمِ فِي الْجَنَّةِ هَكَذَا»
وأشار بالسبابة والوسطى وفرّج بينهما شيئًا.
“Ni da wanda yake kula da maraya za mu kasance a Aljanna kamar haka.”
Annabi ﷺ ya nuna yatsarsa ta farko da ta tsakiya, ya ɗan raba tsakaninsu.
📚 Sahih al-Bukhari
📝 Darasi
Wannan hadisin yana nuna girman falalar kula da marayu, ba sai mutum ya zama mai dukiya sosai ba taimako gwargwadon iko, ciyarwa, tufafi, ilimi da kula da bukatun maraya duk suna daga cikin ayyukan alheri.
🤲 Ya Allah, ka ba mu ikon kula da marayu da masu buƙata, ka karɓi ayyukanmu na alheri, ka sanya mu cikin waɗanda za su kasance tare da Annabi ﷺ a Aljanna. Ameen.
🌿 SABEEL FOUNDATION
Taimakawa Marayu Haske Ga Makomar Su