24/10/2024
Zan kori masu Barace Barace a birnin Tarayya Abuja - Wike.
_________
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya shelanta yaki da barace-barace da yace hakan yana lalata birnin Abujan, tare da haifar da matsalar tsaro.
Wike ya bayyana hakan ne a lokacin da aka ƙaddamar da fara aikin titin hanyar da ta tashi daga Nnamdi Azikiwe Expressway zuwa Judges Quarters, a gundumar Katampe, Abuja a jiya Talata.
Ministan ya ce daukar matakin ya zama dole saboda fargabar cewa Abuja na rikidewa zuwa garin almajirai. A halin yanzu.
“Bari na fadi a fili yanzu, mun shelanta yaki da mabarata saboda Abuja na neman komawa birnin mabarata.
“Idan ka san kana da ‘yar uwa, kana da dan’uwa da ke yawon bara a hanya, ka yi wani abu, domin daga mako mai zuwa, za mu dauke su; za mu fitar da su daga cikin birni.
“Abin kunya ne a ce mutanen da suke kawo ziyara Abuja, abin da s**a fara gani kawai mabarata ne a kan Titin Abuja wannan ba zai yuyu ba ” inji shi. Minista Wike.
Me zaku ce kan hakan?