Barr Hamza Bilya ƙarami

Barr Hamza Bilya ƙarami Hamza Bilya

15/08/2026

Ranan Na shiga Napep, na ciro kuɗi ina irgawa wata yarinya acikin Napep ta fara murmushi wai "La k**an kaine na gani A NTA Ran jumma 'a kuna Programme". Na ce bani bane, Namayar da kuɗina aljihu na sha mur.🤣🤣🤣🤣

25/07/2026

Allah k**a jiharsu ta Jigawa Albarka da Nigeria baki daya Albarkacin Sayyiduna Rasulullah saw

03/04/2026

1.Walau Annahum Fa'alu,
Za su wanku da sabulu,
A lahira baku ba ƙulu.
Sai dai alkhairi da tasbita.

2. Aringa aiki da wa'azin da ake yi,
Jama'a da taƙwa ake yayi.
Shiriya dai Allah zaiyi.
Kuma zai mana wadata.

3. Hanlaza ya ce ya Abubakar,
Ina so in kore munafunci da kyar,
Dan zuciyata tayi karkar
Akan shiriya in tabbata.

4. Abubakar yace masa ai haka,
Munafurcin dai ta zo haka,
To mu tafi gurin Annabin ka.
Mu samu bayani mara karkata.

5. Da za kuci gaba yadda kuke,
A gidajanku ku zama yadda kuke,
A gaba na can yanda kuke,
Da Mala'iku zaku Gaisa ba jinkirta

6.kumu ji tsoron Allah,
Mu gyara duk jumla.
Rayuawan sai la haula.
Kan addini Allah sa mu tabbata.

7. Allah Ninko sallama da Sallati,
Gurin shugaba kamiluzzati,
Almustafa Baba ga fati,
Kamarsa Ga kowa ta tabbat.

@ Barr Hamza Bilya
3/4/2026

03/04/2026

1 .Sun ce zaki mutu Marainiya
In ki Ka rike Namiji da biyayya,
Wannan zance ce yasashiya.

2. Mata ku dena gaba da miji,
Kar a lahira ku yasha yaji,
Ku daidaita akan hanaya.

3.Kiringa Nuna masa soyayya,
Dan Allah ki masa biyayya,
Aringa tsafta inji khairil bariya.

4. Ki dena daukan miji banza,
In kinki ki ran ƙiyama ki sha haza
Ki ɗore akan hanyar shiriya..

5.Yi nayi bari na bari,
A lahira zakuyi sururi
Ki dena sa shi a sarƙakiya.

6.Dole ne ko tausaya Masa,
Allah yace aringa gode masa
Kiyi koyi da shugaban ambiya.

7.Salatin Allah da sallama,
Ga Annabi na mai rahama,
Shine dai khairil bariya.

02/04/2026

1.Rayuwa ba tabbas,
Allah sa Zuciyanmu tai tas,
Mubi koyarwan Ibn Abbas,
Mubi Allah Ba gajiyawa.

2. Suɓul da Ɓaka Allah ka re mu,
Tuntuɓen Harshe Ki yaye mu,
Allah ya fe ma na zunuban mu,
Mu Tabbata kan daidai ba Juyawa.

3. Gaskiya Butulci Bai ba,
Zuciya Baki kyauta ba,
Wannan batu da ba'a taunaba,
Alherin baya adena Mantawa.

4.Aya Jabbaru ya Allah,
Ka cire mu daga wahala,
Talakan ƙasa yayi walwala,
Kaine kaɗai Mai Canjawa.

5.Kar ka yadda Ka manta da jiya,
Don tuwon gobe ake wanke ƙwarya,
Jama'a Lallai Muriƙi gaskiya,
Kada idanuwanmu su zam Rufewa.

6.Allah ya hana Butulci,
Allah Ba yason Ha'inci,
Gaskiya afaɗe ta komai taci,
Jama'a Mu zam masu Ganewa.

7. Shekaru da yawa anyi a tare,
Amma ko zuciya kin share
Duk alkhairan kin ture
Har sun zam abin mantawa

8.Allah Muntuba ka yafe Mana,
Albarkacin Annabi Mai madina,
Shine cikakken abin ƙauna,
Muna Son shi Ba gajiyawa.

9. Sallati Da Sallama gurin Annabi,
Baban fatima mustapa Abin Bi,
Wanda A hallitansa ba aibi,
Annabina Ɗan Larabawa.

hamza bilya,
27/10/2023.

02/04/2026

Masha Allah

Address

Dutse/jos
Jos

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Barr Hamza Bilya ƙarami posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category