Abubakar sadiq

Abubakar sadiq JIBWIS

02/05/2022
07/04/2022
05/04/2022
04/04/2022

SHEIKH ABDULLAHI BALA LAU RAMADAN TAFSIR

Insha Allahu Ta'ala a yau Litinin ne shugaban kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah, Ash-Sheikh Dr Imam Abdullahi Bala Lau zai bude Tafsirin Al-Qur'ani mai girma na wannan wata mai alfarma ta Ramadaan, tare da Alaramma Nasiru Salihu Gwandu.

A jiya idan ba'a manta ba, shehin malamin ya kaddamar da Tafsirin sakataren kungiya Ash-Sheikh Dr Muhammadu Kabiru Haruna Gombe a babban Hedikwatar Izala dake Utako, Abuja.

Za'a bude karatun ne kamar yanda aka saba da misalin karfe 4:30pm zuwa 5:30pm insha Allah, a masallacin Doubeli, Jimeta-Yola, fadar jihar Adamawa.

04/04/2022

Da Na Daina Fadin Gaskiya A Matsayin Liman Gara Na Koma Dako ~ Sheikh Nuru Khalid

Sheikh Nuru Khalid ya mayar da martani kan dakatar da shi daga limanci da kwamitin kula da masallacin rukunin gidajen ƴan majalisu da ke unguwar Apo a Abuja ya yi masa a masallacin sakamakon hudubarsa ta ranar Juma'a da ta tayar da ƙura a Najeriya.

A hirarsa da BBC Hausa malamin ya ce gaskiya ce ya fada a hudubarsa ta Juma'a kuma bai yi nadama ba.

"Idan s**a ce na daina faɗin gaskiya a Najeriya, na daina cewa a daina kashe mutane, to gara na yi dako ya fi mun limanci," in ji Shiekh Nuru Khalid.

Kwamitin Masallacin ƙarƙashin jagorancin Sanata Sa'idu Muhammad Dansadau ya ce ya dakatar da malamin ne daga Limanci saboda hudubarsa ta tunzura jama'a.

"An ɗauki wannan matakin ne saboda hudubar Juma'a ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi zaɓe a 2023 har sai 'yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi."

Amma a martaninsa Sheikh Nuru Khalid ya ce ya yi mamakin da mutumin da ya fito daga Zamfara jihar da har yanzu babu zaman lafiya zai fito ya ce ya dakatar da shi saboda ya yi wa'azi kan hana kashe al'umma.

A cewarsa, kashe kashe bai zama tunzura jama'a ba sai don ya ce talaka ya yi hakuri ya zauna lafiya kada ya fito zaɓe sai an daina kashe rayukan mutane.

Address

Ibadan

Telephone

+2348104368413

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abubakar sadiq posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share