20/03/2026
Sakon Barka da Sallah daga Barrister Usman Saeed Maikeke
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai, ina miƙa sakon Barka da Sallah ga daukacin al’ummar Musulmi yayin da muke bikin Eid al-Fitr bayan kammala azumin watan Ramadan.
Ina roƙon Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana kura-kuranmu, Ya kuma sa wannan rana ta zama ta farin ciki, zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’ummarmu.
A wannan lokaci mai albarka, ina kira ga jama’a da mu ci gaba da kasancewa masu tausayi da taimakon juna, musamman ga marasa galihu, marayu da masu buƙata. Hakan shi ne darasin da watan Ramadan ya koyar da mu.
Allah Ya sa wannan Sallah ta zo mana da alheri, Ya kuma maimaita mana irin ta cikin koshin lafiya, zaman lafiya da wadata.
Barka da Sallah!